
Watariga Lyrics
- Genre:World Music/Folklore
- Year of Release:2018
Lyrics
Watariga - Umar M Sharif
...
Wata ruga, ruga, ruga
Wata ruga
Wata ruga na samo yarinyar fulani
Ta shiga rai, burin da nake muyi aure
Kai na sanar a soyayya zo jani-jani
Wata ruga, zan koma in nayi aure
Soyayya ce, soyayya ce
Soyayya ta gare ki mai riba ce
Nayo nazari kin yimin tantance
Halin mu ya zo daya, haka sa'a ce
Ni na shirya, zani sanya kiyi dariya
Kema ki saka ni in zamo mai cin moriya
Nayi rawar gani cikin soyayya
Tun daga ke a yau na tako hanya
Mu mun chaba mu ake kallo bai daya
Ga yar fillo, gani dan Hausa guri daya
Soyayya taka ce tasa rai na yayi fari
Na kai matsayin da babu mai ce mini in bari
In ba kai ba miya, ina ce maka gishiri
Mai yin kushen ka ni da shi ba sauran shiri
Ai sai murna ga wanda ya cika buri
Kyautar Allah, babu mai maka gori
Duk girman kogi, naga bai kin kari
Na rike mulki, dole inyi kirari
Bani canzawa a son ki nan ne na tsaya
Zo taho tawa fulani ya mai kunya
Kinyi burgewa da shigar ki sam babu haya
Kin rike al'adar ki
Shi ya kara mini son ki
Wataran zamu wuce mataki
Ran da zan zo in biya sadaki
Ki zam iyali na
A kai ki daki na
Ki kare hakki na
Da naki a guna
In zana je gona
Kiyi rakiya gu na
Tunda kayi mini mai zai sa baza nayi ba?
Inda soyayya ba abinda ba za'ayi ba
Zanyi ma damu koda yaushe ba zan gaji ba
Inda rai nasan da rabon mu ba zaya ki ba
Kyan hali ne jarin ka dan Hausa
Tarbiyya na nan a gidan Hausa
Ka iya kalamai na ji tattausa
Ayi auren mu ni fillo na kosa
Wata ruga na samo yarinyar fulani
Ta shiga rai, burin da nake muyi aure
Kai na sanar a soyayya zo jani-jani
Wata ruga, zan koma in nayi aure