Kuduba Girma Irin Na Duniya Lyrics
- Genre:World Music/Folklore
- Year of Release:2018
Lyrics
Kuduba Girma Irin Na Duniya - Umar M Sharif
...
Ku duba girma irin na duniya
Ta taru ne sanadi na soyayya
Kanta akan rasa lafia
Ai fada, a rasa rai har da dukiya
Nima na shigo
Qofa da bubbugo
Kar in zama rago,a soyayya
Kece na hango
Ki biyo ta bango
Soyayya jigo,ku bani hanya.
Gani a kogo,ki bani bargo na sanki in shigo ya zamo lifaya.
Zan rayu dake zan mutu dake abadan dani dake zo mu zauna X2
Zuciyata da taka abokan juna
Da basu rabuwa ko a gun kwana
Ina a farke ko a cikin barci na
Kai nake tunani cikin kwakwalwana
Da wani zaya tsaga jinin dake jikina
Da zaya ga naka yana ta gudana
Akan qaunaaa na manta kaina
Masoyi na nake tunawaaaa
Immmmmmmmmm
Zan rayu dakai zan mutu dake abadan dani dake zo mu zauna X2
Idan nace ke ina nufin ni
Idan nace ni ina nufin ke
Idan nace kai ina nufin ni
Idan nace ni ina nufin kai
Zan rayu dake zan mutu dake abadan dani dake zo mu zauna
Zan rayu dakai zan mutu dake abadan dani dake zo mu zauna
Abadan dani dake zo mu zauna
Zan rayu dake, zan mutu da kai
Abadan dani da kai
Zo mu zauna