Soyayya Ce Lyrics
- Genre:World Music/Folklore
- Year of Release:2018
Lyrics
Soyayya Ce - Umar M Sharif
...
Soyayya ce!
Na yo dace!!
Da nayo kuka yau ya qare...
Soyayya ce!
Nayo dace.
Masoyi bar kuka ni zan share.
Komai yayi mafari ze yo qarshe..
Komai yayi tsauri zaya gusheee
Wanda yake da jari zai sana’a ashee
Wanda ya shuka haquri riba zai kwashe..
Ni jaraba
Yanzu ku duba ,
Ni naci riba..
Qunci ya qare...
Mai imani dole ne za’a jaraba shi.
Har kansq ya kulle , ya gaza bude shi.
In yay haquri a sannu zega sakamakon shi
Misali gani nan zan maye maka gurbin shi.
Zan sa kayi murna.
Kar kayi kuna,
Da kai zan zauna hawaye in share...
Gani a duniya sabuwar rayuwa ta chanza..
Banida damuwa ke kika zo kika min biza
Godiya da yawa bakina gareki ya furtaaa
Kyakyawa masoyiya zuciya ki ta chanzaaa
Na daura baza
Rawa nayi giza
Ina yin shi da izza haushi ya cire..
Dani da kai zamu zam har kwatance
Mata da miji
Haka babban nasara ce
Idan da shaidu ai komai a mutunce
Dun wanda bai so ya gani ransa ya bace
Mu mun dace
Da soyayyace
Mai riba ce qarshen ta da aureeee
Soyayyace
Nayo dace
Da nayi kuka yau ya qare
Soyayya ce
nayo dace
masoyi bar kuka ni zan share
Soyayyace
Nayo dace
Da nayo kuka yau ya qare.