SAURANIYA TA BOYE Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2021
Lyrics
SAURANIYA TA BOYE - Hamisu Breaker
...
Sarauniya ta boye, taken ki zanyi yanzu
Wa zai tsananta kallonki yanzu igiyar shi ta tsiyaye
Kullum ina fada na kara cewa kina a raina
Sam bani manta alkairinki don yayai yawwa a guna
Kaunarki kin dasa min, 'ya'ya ta sunyi huda
Bazan shiru ba nima akanki sai an kira suda
Kaunarki tayi dadi greni zaki ya icen takanda
Kin haka rigiyar sanki tayi zurfi ciki na fada
Bazana gane kaina ba sai kin zaman icen kirya
Ba na fadi bane tunda komai a kanki na shirya
Ina sanki so na hakika dake mu hau hanya
Idan kina tinanina ina naki ne cikin duniya
Nidin ga naki ne, in babu ke a kirani da maraya
Ina yawwan fadar hakan akanki nake kara kyauta halaiya
Kinji masoyiya
In babu ke cikin duniya ina zana je ni don kwana
Ina gatayi kinji ban san ki furta bankwana
Sirrin dake rai na baki zan rike ki da amana
Ko banyi miki dai dai ba
Ni dai kawai abunda nasani ina sanki tunda nagano
Kema ki furta kin yarda basan na dinga konono
Kowa yana fadar ke kike gu da anga na kun no
Mai kyan sufa da kyan aiba
Kice adon gari tunda kin saba zarce yan mata
Sanan sinadarina da barki walla nai wauta
Ke nai wa tanadina cikin duniya ina fata
Kin ce bazanyi rauni ba
Ina yawaita zance ki bana dare bare rana
Ki tausaya garan karki bar zuciya cikin kuna
Nasan kina sane tunda na bayyana tinanina
Mai sanki nake yar baba