Nagane Duniya Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2020
Lyrics
Nagane Duniya - Hamisu Breaker
...
Ni na gane duniya sai da masoyi ake zama kalau
sanan naji duniya gun mai kaunarka zaka ce salam
Abin duniya quddusun fanna'un kmr kidan halam
to nima masoyiyaa zan bayyana miki ina zama kalau
to jirgin masoya zaka wuce zo ka karbi sakona
Dan na tara gayya wasiku ne zaka kaiwa mai so na
wayyoni rayuwa idan da masoyi tana yawan dadi
Idan an rabo da juna wahala zata tashi mai fadi
Adan baka tablet a baka ruwa Amma basu ma dadi
zancen mazan jiyaa akan so ne ko ince da ku tadi
kifin cikin Ruwa yasan ina sonki jarumar mata
Sirrai da tsaunika sun shaida kin shigo tunanina
idan nai farin ciki ai kice sannadin sa ba haufi
idan nai bakin ciki kicemini in zo gidan ku ma yafi
kidan bani tallafi domin kaunar ki tayi min zurfi
A Domin guje kishi mubar gulbi kinga faddama yafi
kidan daina tantama indai kaunar ki ce ake nabi
Dukkan abinda zuciyar ka ta so to yana hannun dama
kin yarda ynxu na narke to zakiminni alfarma
ki taso muje gabbas miyi addua dan mu samu yar dama
mu kore bakin cikin mu samo fitila mu haskake kowa
sanan mu dan dana mai zaki ne sai mu ba kowa
Da ni da kee masoyiya zamu hidimtaawa.so kwaraikwarai
dukka abinda da zana ce yazama kinji shi babu so na rai
Fahimtar ki ce ta sanya.....
Na so ki soo na tara gayyaaa....
bakina yayi kadan in bayyana yanda kaunar ki tai a zuciya
Sai dai in yi miki albishir da kece ado nawa duk gaba daya
wa'aniyar ki fara yana ya
ki minni halinki nima na koya