Karnin Sabo Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2020
Lyrics
Karnin Sabo - Hamisu Breaker
...
yanzu karnin saboo,ya tsinkaye ni
kuma nau'in kaunaa ya rinjaye ni
yanzu karnin saboo,ya rinjaye ni
kuma nauin kaunaa ya rinjaye ni
zuciya ta darsuuu,da sonki har ta gamsuu,kunnuwan ki rufe suu
kar zuga ta taba suu.
kinga ni dai kin mini ke ma ki zayyanar in nai miki
ki tausaya ki cire mini shinge a zuciya ba shamaki,dukkan masoyi bazaya so bankwana ba masoyiyata.
To kaunar ka dai tayi rassai har tsinka nakeyi a zaune,mahadin ta so ne
kullum sonka ke kwankwasa mini kofar zuci yai sallama ne,akan martaba ne
buri na zaman lafiya,kai na kusan ta mai tarbiya
dukka dare zuwa safiya ina kallon ka ne tun jiya
kalamai tuttudowa suke,suna yi mun kawanye suke
muddin zaki nesanta zan jure a'a tuba na ke
ina kallon ka tamkar chida,ina shaidar ka har abada
abunda nake tunani zaman mu zai tsoratta yan hassada
ni dai sonki ya fi mini
nai laifi ki yafe mini
kar ki guje ni dan yanzu na saba son ki ya far mini
abin kauna abin marmari
akanka nake ta karin shiri
domin dai na burge ka tunda gaskiya ba ta neman tuni
wayyo sonki yay mamaya
yay girma kamar maliya
wanda ya kalli mai so ya bar shi nan haka bai zaman duniya
akan ka na koyi karfin hali
zan yafe in sa kwal kwali
dukkan macen da tai kokarin taba mini kai akwai jan hali
kinga shigar ki ta dau ido
irin kayanki ne na ado
ni shauki nake in na kalli mai so na idan ta fito
abin so na abin tutiya
nai damara ga ke na tsaya
wanda ya so ka zan so shi tunda so ne garkuwar duniya.