Na Taka kaya Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2022
Lyrics
Na Taka kaya - Auta Waziri
...
Auta Waziri kuke ji malam
Prince production
(Prince production)
Kin sace zuciya
Kece sarauniya
Koh in kira ki gimbiya
A kanki ban duba dukiya
Dan ita dukiya, bata kai ya zuciya ba
Na taka kaya
Masoyiya zanso ki tsaya
Koh ba magana, ki gane so ne zana biya
Na taka kaya
Masoyiya zanso ki tsaya
Koh ba magana, ki gane so ne zana biya
Na taka (na taka kaya masoyiya)
Na taka kaya
Na taka kaya
Dan Allah dan zo ki cire mun
Dan bar tafiya, masoyiya zanso ki tsaya kiji
Ciwo da dafi, kamar abun sai an masa agaji
Nisan tafiya, a kanki kinsan bai sa in gaji
Zanso ki tsaya, sauti na muryar taki kawai naji
Na lasa zuma, amma zumar so ne kisani gwanata
Na taka (na taka kaya masoyiya)
Na taka kaya
Na taka kaya
Dan Allah dan zo ki cire mun
A kace sabo tirken wawa ga ƙarshen magana
Inda zaki tina, in kika barni akwai fitina
Kece wace na baiwa makulin zuciya adana
In har kika bari, wasu sukai barna a ciki da sake
Na taka (na taka kaya masoyiyata)
Na taka kaya
Na taka kaya
Dan Allah dan zo ki cire mun
Na taka kaya
Na taka kaya
Na taka kaya
Dan Allah dan zo ki cire mun
Shi mai so da makanta yazo sai dan rakiya
Kuma dan rakiyan komai ya siya shi zaya biya
A silar soyayya dai ake jure tafiya
Inko ta ritsa sai aci gaya babu miya
Wani sa'in ma sai kaji mai so yai aniya
Wai zaya bari, zai daina kuma bashi iyawa
Na taka (na taka kaya masoyiya)
Na taka kaya
Na taka kaya
Dan Allah dan zo ki cire mun
Shi fah so da dadi batu na zahiri
Bashi duba talakawa ko attajiri
Fari ba a gane na kirki da makiri
Sai a hankali, so zaya bayyana
Na taka kaya
Na taka kaya
Na taka kaya
Dan Allah dan zo ki cire mun
Mahmud MG on the mix