Autar Mata Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2022
Lyrics
Autar Mata - Auta Waziri
...
Auta Waziri kuke ji Malaannn
Kuzo kuji ga autar mata
Karku taba mini yar gata
Ku barni kawai nayi mata rawa
Babu irinta cikin mata
Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Ku barni kawai nayi masa rawa
Babu irin sa cikin su maza
Autar Mataaa….
Kuzo kuji ga autar mata
Zaki na zuma baya illa
Naji tun farko
Bara na zube muku labari
Da na dan dauko
Da na tsunduma kogin soyayya
Nayi linkayaaa
Na hadu da ya mai Alkunya
A daren farko
Mun shaku da ita a soyayya
Ba ja baya
Abun da take so ta nuna
Kuma na dauko
Ku barni kawai ni nayi nisa
Sonta jiki na yayi rassa
Babbar maganar ma nayi bacci
A mafarki na naga mun aure
Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Ku barni kawai nayi masa rawa
Babu irin sa cikin su maza
Autar Maata…..
Kuzo kuji ga autar mata
Abun da nake so ka bani
Baka mun karya
Gare ni ka zamma cikon buri(Autar Mata)
Ka rike matakan soyayya
Kai baka zarya
To dole a saka a tarihi (Autar mata)
A rai ka dasa mini soyayya
Kai daya ne da guri
Gare ka nake dada tambihi( Autar Mata)
Gare ni ka zamto Alkhairi
Da bai manta Uwa
A barni da kai muyi soyayya
Kar muyi yo rabuwa
Kuzo kuji ga autar mata
Karku taba mini yar gata
Ku barni kawai nayi mata rawa
Babu irinta cikin mata
Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Ku barni kawai nayi masa rawa
Babu irin sa cikin su maza
Autar Mata……
Ku zo kuji ga autar mata
Sabo da maza akace jari
Na san kin gano
Ke zaki kure su a labari
Samun mace ince tamkar ki
Alkhairi ne ma
Ki kauda dukan wani me sharri
Kowa ya fada miki zai so ki
Sam bai kaiwa ni
Haka in yake ba wani inkari
Na bar magana in ba hujja
So baya tabuwa
Me yinsa yake masa linzami
Dan kar ayi rabuwa
Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Ku barni kawai nayi masa rawa
Babu irin sa cikin su maza
Autar Mata…..
Ku zo kuji ga autar mata
Ka ce mini zamuyi soyayya
Tun haduwar farko
Amsa maka nayi ba jayayyya (Autar mata)
Kawaye na sunyi mamaki
Yadda na dan sauko
Ta yadda na amsa na shirya (Autar mata)
Abin da ya sa naji zan so ka
Kayi zubin natsuwa
Na bincika kyawun halayya (Autar Mata)
Bara na rufe maka labari
Sai da mukayi shakuwa
Na gane ana gina soyayya
Har tayi daduwa
Ku zo kuji ga autar mata
Karku taba mini yar gata
Ku barni kawai nayi mata rawa
Babu irinta cikin mata
Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Ku barni kawai nayi masa rawa
Babu irin sa cikin su maza
Autar Mata…….
Ku zo kuji ga autar mata…