Hafsa Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2020
Lyrics
Hafsa - Ali Jita
...
..............
Hafsa kunga sarauta ce da gaske
Hafsa yau jita ke nayi wa wake
Hafsa tashi ki taka nan a take
Zuciya da amana hafsa dauke
Zuciyar mai ciwo hafsa wanke
In duhu ya ratsa hafsa haske
Mai abin mamaki hafsa kenan
Mai karatun boko malamar nan
Gun rikon addini hafsa na nan
Mai masoya da yawa jarumar nan
Tashi hafsa ki juya ba irinki
Kai nuwa daga Allah yaifa saki
Mai fada da cikawa Ina kiran ki
Ko cikin danginki ana yabaki
Daukaka daga Allah yana daga ki
Tun kina yarinya irin halin ki
Yanxu xana yi waka ta gimbiyar mata
Hafsa mai alkhairi ke kiranta
Mai rawa kayi rawa ina kidan ta
Zamani ne nata ina yabata
An gwada an gane bata cuta
Bata kallon makiya in sun taba ta
An buga an barta yanxu gata
Dogaron ta da Allah ya tsare ta
Walkiya ta haska bangaren ta
Munga hasken hafsa mai zumunta
Ko ruwa ya kawo zai tsaya ta
Baya cinye hafsa baya shan ta
Ko wuta ta kama ta kashe ta
Gaskiya ce doki ta rike ta
Duk kadangar sharri ta tare ta
Zuciyar alkhairi ne nufin ta
Mai rubutu ita yau zai rubuta
Mai karatu hafsa zai karanta
Hafsa ba matar yara bace ba
Hafsa ba maganar karya take ba
Hafsa ba layin boka take ba
Hafsa ai ba mummuna bace ba
Hafsa ba kin al'umma take ba
Amsa sunan ba wasa bane ba
Tunda ba kowa za'ayi kira ba
Sai su wance da wance kunji babba
Yanxu jirgin sama yazo ya sauka
Hafsa shiyayi niya zaya dauka
Gashi jirgin ruwa yazo iyaka
Hafsa shi zaii sauke bata tamka
Sannu baiwar Allah hafsa kenan
Rayuwa tayi kyawu duniyan nan
.......................