Rashin Masoyi Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2013
Lyrics
Rashin Masoyi - Nura M. Inuwa
...
Rashin masoyi baida dadi nai takaicin huce haushi
Idaniya ta nata kuka so ya cinman ban zato ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dai kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
Da marmari so kamar da wasa so yake shiga zuciya ya zauna
Yana da kyau duk abinda zamuyi mu dinga nazari mu auna
Kunji labarina nidai zakusan ni naiwa kaina
Danasan haka tun a farko aninda nai ni bazanayo ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dai kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
Na 'dau ki hanya na tafi zanaje gun masoyiya ta
Naci ado na sanya kaya ita dai naiwa kwalliya ta
Idan naje sai naga abokina kunga dole ne nai fusata
Sai na hau dokin zuciya ban tsaya naji ba'asi ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dai kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
Sai ta biyo ni tana kirana nai biris ban waiwaya ba
Sannu ta durkusa gabana katsaya ka duba
Kai kadai ne a zuciya ta wani bazanyo na'am dashi ba
Ga hawaye yana zuba Fuskar ta ninban kula dashi ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dai kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
Sai nace kin saba dani a wanga rana zana barki
Gabanki ciwon zuciya ta zana koma gun 'kawar ki
Sai tace kada zuciya tasaka kaiman wanga aiki
Amma jeka babu komai ba ja-in-ja zamuyo dakai ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dai kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dau kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
Umm daga nan sai na tafi nabarta a cikin wanga hali
Gobe in zance ya tashi ai dani zatayo misali
Sai naje na iske 'kawar ta so da 'kauna mukayi 'kulli
Tayi nuni naso a fili batayiman har a zuciya ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dai kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
Ashe ita tin daga nan ciwo take ba'a san dashi ba
Gashi tayi zurfin ciki ko a gidan sam bata fada ba
Kai har ta turo man da sako tace nazo nace bazana zo ba
Tinda dai kunga babu yinta sakar ta bazata war-ware ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dai kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
Um zaune nake ina nazari sai naga ankawon wasika
Guda biyu daban daban na rasa wacce zana 'dauka
Sai na fara 'daukar 'daya na duba wai miye anka saka
Sako ne daga 'dayar budurwata wai bazatai aure dani ba
Rashin masoyi baida dadi kabar takaicin huce haushi
Tinda dai kai kajawa kanka bakaji dadin rayuwa ba
A 'dayar aka ce dani nasanya ciwo na so a zuci
Aka gargadan karda na zargi aboki 'dan asali na Bauchi
Sannan tanayin takaici tinda na rasa yin azanci
Wai da ciwo zata tafi bata san inda zataje ba