Salma Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2015
Lyrics
Salma - Nura M. Inuwa
...
Bankwana nake ma masoyina na tafi sai wataran
Bankwana nake ma masoyina na tafi sai wataran
Yau ku fito da labari nazo
Idanuwa na na ta ganin hazo
Nai godiya ga duk yan gwangwaxo domin ban raina kalar su ba
A gaskiya nasha wahala ta so
Sirri na zuciya zan fallaso
Ta sami rangwame na rage kaso kauna bazan daina ta ba
Na fara so ina da kuruciya
Tun daga so ya darsu a zuciya
Sai hankali ya bar yin kwanciya ga so bansan launin sa ba
Mun tashi tare ne a gida daya
In an aike ta ni naka rakkiya
Ko watara naje ita tatstsaya amma bason ruhinmu ba
A hakane mukeyin rayuwa
Domin kasantuwar mu na yan uwa
Tana fadin in zammata garkuwa baza naso a raba muba
Kwana a tashi sai girma muke
In na tuno ta har kuka nake
Kauna da sonta in muka farrake wani gun baza na rasa su ba
Domin a junanmu da alkawar
Mun hana zuciyoyi sukkawar
Ko babu salma in nayi tsuntuwar kauna bazan dauke ta ba
Kullum akwai gurin da muke zama
Junanmu muyi tayiwa tuhhuma
In munyi makkaranta mun gama aure bazamu ki yinsa ba
Sannan ta dauki zobe tassakan
Tace alkawari na rike kan
Zan dawwamawa ruhina dukkan kauna bazan manta ta ba
Gobe da safe zasuyi taffiya
Gashi gari anayin walkiya
Sai ta wuce tana yin dariya yanayin dani ban gamsu ba
Nace da ita dai tayi hakkuri
Ga yan kudi kadan tayi guzziri
Ni dai tazon da kayan marmari su naffiso gun tsarraba
Cikin mafarki salma tazo mini
Tace dani tazo ta sanar dani
In ta wuce a yadda take gani bai zamma dole mu haddu ba
Ai tafiya ba mutuwa bace
Yadda na bata amsa ta bace
Sannan na tashi nayi addua nace Allah yasa ba gaske ba
Da asuba suka zuba sammako
Ni kuma zuciya ta na dako
Ga makara tasa ni rashin rako har sun wuce bamu haddu ba
Da ko na tashi nai maza naffito
Suna na salma shi naka ambato
Ya kika barni kinkai sakkwato bake ni bazan rayu ba
Mutan gidanmu na ta haniya
Ni tausayi nake na kuruciya
Kada mafarki yazzama gaskiya hankali na ba zai samu ba
Na koma daki nai shiru
Ba zama ina ta wuruwuru
Salma ko tana hanyar zuru raina ina yin fargaba
Sai na jiyo bugun kofar gida
A yanayin garin dai ga cida
Sai na taho bana duban gada nai tuntube ban lura ba
Ina zuwa naga wassu mukai hannu
Suka ce sunzo da maganganu
Tunda na gansu nacce na banu basu faddi sakon naji ba
Da suka ce mota tai haddari
Take najji ni ina jiri
Sunce muje kawai ba jinkri
Jama'ar ciki basu rayu ba.
Koda naje nagga masoyiya
Salma mai kyau ga kwalliya
Kwance bata motsi duniya a idona hawaye yai zuba.
Aka zo aka shirya ta tsaf
Sai nazo na zauna gani daf
Domin kwa ansani mun shaku kaf baza na jure rashin ta ba.
An mata salla nan ni kuma
Na roki sarki Allah mai sama
Domin yayi mata rahhama roko bazan daina shi ba.
Tun daga nan na yanke shawara
Na daina so na hakkura
Don kuwa salma yarinya fara ba zana san madadinta ba