
Makamashi Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2023
This song is not currently available in your region.
Try the alternative versions below.
Alternative versions:
Lyrics
Makamashi - Namenj
...
Namenj…
Harshe na tokar sashe na
Zafiransa yayi luf luf bisa kaina
Dashi naje nayi bankwana
Babu shi cikin rai har qalbina
Dashe na so yayi yabanya
Inuwa ta ganyen dole ta sanya
Ta sa sukuni ga masoya
Inuwa ta ganyen in sun zauna
Masoyiya la-le la-le
Muje gida gaida iyaye
Masoyina duba duba
Qaunar ka tasani tsumayi
Idan kina wannan zance kamar na zubda da hawaye,hawaye, hawaye
Makamashin rurin qauna
Yayi garwashi zai qone raina
Ka taimaka linzamina
Zo ka agaza ya mai begena
Ka bani zobenka masoyi
Insaka a hannuna zan juyi
Akanka ni bana shayi
Alqawar nadauka ni zan nuna
Tininiqi kesa shayi
Shimfida ta qauna karki sauyi
Kwalangwaso ni banayi
Manufar dake raina zan nuna
Masoyiya la-le la-le
Muje gida gaida iyaye
Masoyina duba duba
Qaunarka tasani tsumayi
Idan kina wannan zancen kamar na ni zubda da hawaye,hawaye,hawaye
Makamashin rurin qauna
Yayi garwashi ze qone raina
Ki temaka ya mai sona
Zoki agaza ya mai begena,begena,begena
I say begena,begenaa…..