
KO ZA A FASA Lyrics
- Genre:Alté
- Year of Release:2021
Lyrics
KO ZA A FASA - Abdul D One
...
Rahman boy youngest producer
ko za'a fasa baza na daina ba nai miki don gaskiya akan kauna
Ni ne Malaminki mai fassarar mafarki
abin da ya shafi zuciyar ki nan kaɗai nake aiki
a magance matsaloli na soyayya na zamo sarki har fadawa garen a cikin so ina da jayaki
ita ce zuciya wacce kullum da ita ake aiki
da babu soyayya duniyar bata zama dai-dai
ehh mai girma kake ba iya kasa ba da tsallake don kowa kake wacce ta rasa kuka take in ka iso garen ji nake kamar Giwa nake bana fatar koda yaushe a mai hidima nake daɗaɗɗan kalamai nasa gabobi su sake nawa fari tatas mai kama da kyawawa kake
karfin duniya an kirkiri soyayya an sakata a zuciya nazama ke kin zama Ni mun zagaye ko'ina Allah sai muyi godiya
Mai rubutu ne Ni, mai zane Ni, siffofin ki zan zana suyi dai-dai
a cikin jini naji kai din Dan uwa na ne
DNA Dina da naka an auna dai-dai ne a cikin gida in ka duba sunanka na zazzane ka shiga jikina ka chanza duk siffofina ne ajiye maganar baki zuciya ita ke aiki ba batun wani mai raki komai nawa gyarawa kake