Hakkin So Lyrics
- Genre:Afrobeat
- Year of Release:2024
Lyrics
Hakkin So - Salim Smart
...
Salim smart on the beat
Ahh, ba kowa zai gane ba
Yanda ake Jin zugi
Indai har so ya darsu koh kuma yai maka barna
Ni kam so yai mini barna
Ya chanja mun suffana
Ya mai san tamkar bare a cikin dangina
Ya sauyan lissafina
Ya tauye mini hakki na
Yasa na baje sirrina
Sumbatun soyayya shin menene ke jawowa
Yaudara ce ko kuma kula ku ban amsata
Amma wani sa'in zuciya ta ce ke harbawa
In na tuna cewa a soyayya nayo bauta
Wasu har sun chanja mini kallona
Sun kasa su gano meke damuna
Ni daya nasan menene ciwona
Magani nasa Allah daya ne gata na
Ehh, inna mutu kaine sanadi
Sannan kuma baka da madadi
Samun mace mai kaunar ka kamarni ba lallai ba
Hanyar daka nunan zana bi
A silar so nai maka ladabi
Amma haka bai sanya ka tunanin fasa butulci ba
Menene soyayya inba karya ce ba
Menene soyayya in ba cuta ce ba
Menene soyayya inba hadari ce ba
Na raina na huta harkarshen ra'ayi na
Yaya zakayi da hakkin soyayyata
Ka saba mini da so kuma kai mun keta
Ka barni alaka tamu ka yanke ta
Ka mamaye sashin zuciya ka chanja ta
Ko wani laifi nayi ma ne? Ban roki ka yafemun ba
Domin na horu da soyayyarka tun ban saba ba
Yau kuka gobe kuka ni dai bazan jure ba
Tunda Allah na nan addua ce zatayi gadi na