Fadli Lyrics
- Genre:Afrobeat
- Year of Release:2018
This song is not currently available in your region.
Lyrics
Fadli - Umar M Shareef
...
Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya
Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa
Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya
Ciki na samo ka nayi nasara a so ba damuwa
Ba zan so ba, koda wasa bazan barki ba
Na duba, a ciki ni banga kamar ki ba
Mun saba, ni da ke ba za'a raba mu ba
Mun caba, in akayi aure munyo gaba
Shine daidai tun daga nan mu bar yin fargaba
Ke na so tunda ni kika so hakan ne kyautuwa
Kai ne farko, kai na cira cikin su mazan gari
Mai karko, wanda bai sanya ni inyo jiri
Muyi baiko, ni da kai tun tuntuni nayi shiri
Da ka aiko, iyaye sai ayyiri-yiri
A cikin auren nayi shiri na daukan hakuri
Na yarda da kai zan zauna iyakar rayuwa
Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya
Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa
Lallai, kauna ce da so, kin nuna gare ni
Ko anki ni so, kece mai kula ni
Nayi dace a so, abokai na kuji ni
Ke nafi so a so, in an tambaye ni
Bana kallon kowacce 'ya cikin yanayi na so
In ba ke ba banda abokiyar yin rayuwa
So na dandana, zaki ya rufe ni
In na rissina, masoyi na daga ni
Ni zan adana, sirri in ka bani
Naki in bayyana, ko an takura ni
Sam ba kowa idanu ba wanda suke gani
Kai ne dai wanda tun asali muka yo shakuwa
Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya
Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa
Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya
Ciki na samo ka nayi nasara a so ba damuwa