Rariya Lyrics
- Genre:Pop
- Year of Release:2016
Lyrics
Rariya - Umar. M. Shareef
...
Tankaɗe dole sai da rariyaaaaaaa
Rariya × 6
Tankaɗe na yau na sa rariya, kece kika zam tsaba, zaɓina a soyayya.
Tankaɗe na yau na sa rariya, kaine ka zamo tsaba, zaɓina a soyayya.
Na tankaɗe soyayya ta na sa rariya rariya, dan in guji cuta Allah ne mai kariya kariya, kuma na dace don na samo mai tarbiyya tarbiyya, lafuzanta da daɗi sam-sam bata ashariya shariya, na zam gwaninso dole a yi mini jiniyaaaa, in na taho ki yo ɗauki, ki min tarba ta soyayya.
Rariya rariya
Nan nan nan nan nayi nisa a so, nayi ƙololuwa loluwa, cikin kala daminnan nayi yo tsintuwa tsintuwa, kai ka zame mini allura na cikin ruwa cikin ruwa, na zama mai sa'a samunka a rayuwa rayuwa, duniyata yau ta dawo sabuwaaa, kai ka shigo ka yo aiki dole in maka sakayya.
Rariya rariya
Aiya ahh, ruwan sama in kaga yayi zubowa, ai damina ce, aure in kaga yayi ɗaurewa wannan ƙauna ce, kyautar Allah na da yawa na ga, baiwa baiwa ce, Shi Ya haɗamu da ke kan ƙauna an ce mun dace, in na rasa ki a soyayya sai na maceee, Ko ko jiki ya bar aiki tunda rabinshi ya tsaya.
Rariya rariya
A hagu da dama kai naka dubi, na faɗawa iyaye kaine zaɓi, littafin so ciki babi babi, sunanka yana ciki fannin hubbi, kowa ka gani acikin littafin ga niii, dole hanunsa bai mulki ko ko sarautar soyayya.