KO DA KUDI KO BABU ANNABI NE SAMAN DUK HALITTAR ALLAH Lyrics
- Genre:Reggae
- Year of Release:2024
Lyrics
Ko da kudi ko ba kudi
Indai da Annabi
Shikenan
Annabi ne saman duk halittar Allah
Banji tamkar yashiba
Almuhiyi iyamin na dora
Ban damarka allah tabara
Zanyi abinda kaine ka fara
In ka aminta bazan gazaba
Kara dubun salati mujibu
Ga wanda gunka yazam habibu
Wanda muke ta nuna wa hubbu
Bumu san randa zamu bari ba
Sa ahlai kasa har suhabu
Sa shurafa jinin mahabubu
Gaida uwa darai koko babu
Zan tafi zanyi bazan tsaya ba
Kece asalin zuciyar sa
Tsokar shugaba tajikin sa
Umma abunda raina ya kun sa
In na bida bazaki hana ba
Cikin ladab da kas dakai na fara
Annabi ganinan ba dabara
Sai tsantsa ta kaunarka nura
Mai hasken da ba zai gushe ba
Kafi gaban sanin duk halitta
Balle ma baki ya furta
Annabi kai kadai ka dayan ta
Allah baiyi tamkar ya kai ba
Komai daga shi muka samu
In mun roki Allah ya bamu
Sai munzo dakai ya imamu
Sannan rabbana zaiyi duba
Maiwa kaunu mai yiwa Allah
Kai ka sanar damu rabbu Allah
Badan kaiba wallahi Allah
Da baa san akwai rabbana ba
Jeka abinka rainon halima
Muko mudinga yima walima
Tilas kaunu tassalama ma
Bayan kai baayiyo gwani
Ko musa dakai aka bashi
Isah sai dakai aka sanshi
Kyan yusuf ko kaine ba bashi
Allah baiyi ma kishiya ba
Ban tabajin kamar shugaba ba
Gun girma baayo yashiba
Kai bari buncike karka duba
Baza ka san kamar shugaba ba
Nai nazari kadan take nace
Ko tafiyar sa ma ta daban ce
Cif cif yake ga kwatance
Komai nasa ba namu neba
Ga hasken hakora gareshi
Da ya taho guri kaji kamshi
Dole na raira baiti gareshi
Nayi ta fada baayiyo yashiba
Suyi masa sharri yayi musu khairi
Mai kyautar da sam baya gori
Kai kusa sani ashe rai da buri
Buri na yayimin maraba
Ce na taho ziyara madina
Inzo gunka ya dan amina
Dan fadima cene na zauna
Na roka bazaka gaza ba
Zana takaita baitin na huta
Koda da tambayar wanda yayi ta
Sunusi piano zoo road yayi ta
Ni da hubbu ba wani ne ba
To aikin ka ne zuljalu
Kara dubu dubu gun salahu
Wanda ya zarce kowa a sulhu
Abban fadima mahabuba
Karshe addu a ta ka amsa
Duk makiyan mu sasu su kasa
Duk mai sharri komar shi kansa
Barmu da sayyada umma abba