JIGO Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2024
Lyrics
S Piano on the beat
Shi Shine
Daure gareni sahibi ka zamo mini jigo
Na tabbata kai daya ne zaka zamo mini bango
Matso gareni karka gujeni da dogon zango
Dan zuciya ta kai daya ke burin ta hango
Ka tausaya min karda ka furtan kalmar a a
Gamo dakai na tabbata nayi babbar sa a
Ka tausaya min naga gareka akwai da a
Ka karbi soyayya ta
Daure ka dan sassauta
Ka tausaya wa ruhina
Ehh
Dashen da kayyiwa zuciya sam bazai warke ba
Kalma guda in kayi min bazai wuce kaimin fami ba
Zauna a dama na dan kallon ka bazan qosa ba
Idan kayo nesa dani bazai hana in qoka ba
Ayyi riri bidiri yau nawan ya cire tuta
Cikin mazaje ni in na duba ya banbanta
Koda shigarsa daban take yayi kalar ajebota
Wayyo ni naci gari
Taho kajani muje alkawari sam ni bazan yada ba
Ehh yaushe kake da bukatar asa amarya lalle
Cene dasu Ni Taka ce Na Zamto Ma Yar Lele
Cikin Gidan Ka Ka sani Kasa Sakata Maza Kulle
Zigar Magauta Kar Ka Biye Musu ni Zanso Kwale
Mai mini Gata Mai Daukar Dawainiya ta Kaine
Da nayi Fushi Mai Sani Nishadi Kai Kai Daya ne
Da Na Kira ka Habibi Ko Hubbi daidai ne
A zuciya ta kai dai nayiwa gurbi Zo zauna