Taurarona Lyrics
- Genre:New Age
- Year of Release:2023
Lyrics
Taurarona - Hairat Abdullahi
...
Salim Smart on the beat
A hasashe soyayyace farkon kowa
A tunani na kuma ta zama dadin kowa
Sanadi ce ta halittar duk wani bawa
Makasudi ta zuwan mu cikin duniya
Yau na samu nawa
Mai kyawun nunawa
Tauraro mai haskawa
Mai sa nai darawa
Oh-oh-oh-oh-oh, oh-oh-oh-oh-oh ohh
Uhm hmm
Uhm
Wa zanso inba kaiba
Wa zan aura ba kaiba
A kaunar ka na sa damba
Rabuwar mu da kai ba yanzun ba
Haka za su ganmu, kuma su barmu
Tunda Allah yayi hadawa-ha-ha
Abin kauna, ango na
Alfaharina, sirrina
Aminina, jigona
Mai sanya min natsuwa
Kai sarki ne mai mulkin masarautar zuciya
Kai sadauki ne mai yaki da illar soyayya
Zan aureka na shirya
Muyi zaman mu har abada-ha-ha
Oh-oh-oh-oh-oh