Haske Lyrics
- Genre:Spoken Word
- Year of Release:2024
Lyrics
Haske
Da tsantsar duhu ake sanin mahinmmancin haske
Iko dai Allah ya bamu
Matasa masu kwazo
Kuma ya kasan ce halali da wuyan samu
Ido a rufe amma fata muke mu ga haske
Cin hanci gabas da kudu
Wannan al'adar ba ta mu bace to ta ya za'a yi mu ga haske
Abun da kunne ya ki ji ido na gani
Wai wai wai
Toh shin Ina lefin manomi dangin manoma
Da daga sitirar sa, ci da shan iyali duk shi ya noma
Manoman da ba hadin shi da kisisina da lakumashen duniya
Aka saka a tsakiyar wannan harkar kissina ta yan duniya
Toh
In manomi ya rasa abun ci daga ina zamu ga haske
Da sannyin safe ake kama fara
Gashi Fargaban tashi ake da safe
Yadda zata fara ake sani yadda kuma zata kare
Toh
Wa ya sani
Allah gamu gare ka
Ko barawo kamata fata yake a samu
Ko ya samu abun da zai sata
Allah gamu gare ka
Hannun mata ya dade rike da sanao'i
Kudin adashe ya koma hannun likitoci
Abun sulella ya harba miliyoyi
Fargaba kan fargaba
Haske
Ina kike kanwata, babbar diya ta
Yar gaban goshin uwar gida ta
Bidar ki muke yar gata
Bidar ki muke yar gata
Haske
Kar ki yaye mu
Kowa ya bar gida, gida ta bar shi
Amma ina mu ina ja da ke haske
Bidar ki muke yar gata
Bidar ke muke yar baba
Haske