
Good Morning Lyrics
- Genre:Hip Hop & Rap
- Year of Release:2023
Lyrics
Good Morning - Kossy
...
Big shoutout to dj abdul eh
Kossy
Dan talaka I see you
Aka mai bakin gaskiya
Wanda baya karya sosai
Ashigo da kujera 3X
Freestyle session part2
Yho yho yho
Lots go
Allah sarki duniya kamar da wasa yanzu gashi
Shekaru ashirin da biyu hammata ta da gashi
Kalu bale na rayuwa ci karo da fadi tashi
But babana yace mini habu inka fadi tashi
Wannan maganar nakan tinata sau uku arana
Dana tina sai inji sanyi koda ina a rana
Lokuta da dama nakan rasa ci dasha a rana
Amma yanzu kunga nafi karfin duk abun arana
Yace kome zakai cikin ranka kasaka su ali
Yau zan sakaka makaranta tashi kabi su ali
Ilimi a gurin mutum shine cika da kamala
Ga misali mana zoka duba musa da kamala
To da wannan daman nakeso in danyi tunatarwa
Niba malami ba amma yau ni zanyi fadakarwa
Matasanmu da yawa dake shirin tabarbarewa
Na daura kambu a hannu na zanyi tseratarwa
Ina kwana an tashi lafiya ina gajiya
Fatan ganin gobe lafiya yadda mukaga jiya
Toh yi bada kyauba kuskure mun baroshi a jiya
Dan cikar muradi lokacinsa ne ribar a jiya
Dakko tawada alkalami sannan kazo ka zauna
Ina fada kana fada nasararmu saika zana
Nima dan adam ne ajizi inada nakasa na
Amma hakan baya zugani in tauye na kasa na
Zan danyi tsokaci akan abunda ke wakana
Zanyi tini akan fadin mutanen dake gabana
Masu aminta da juna masu riko da amana
Alasa sakon ya kaiwa mutan baya da gabana
Saimu furfuto da hanzari domin mu kama fara
Karkaji tsoron ganin karshensa kawai dai kafara
Domin yau da gobe ta zarce ayi mata dabara
Inka duba zakaga bambamci da bana da bara
To a dunga waiwayen na baya ne ribar tafiya
Damu da abunda ke gabanka banda interfere
Though I was born a super man haka inji iya
To amma tace you have to very learn kafin ka iya
Abaya ka tsinci kanka a hali matsananci
Kana ganin cewa kafi kowa zama matalauci
Shawarar dake zuwa a kanka zama mabaraci
To koka manta da cewa mahakurci mawadaci
Kodadai wasu da yawa a cikinmu sunbi yayi
Sun manta da cewa rabbi allah shine mabuwayi
Rabonka baze taba wuceka ba kawai bi layi
Zaka gansu akan layi haka sunata bulayi
Wai leaders of tomorrow shey you know we are the future
I am graduated how am I become a teacher
After all the forthcoming things im sure na we go lunch am
To idan hakan ka dauka wallahi kayi chacha
Masu raina abunyi ciki sune jiga jiganmu
Da burin kudi da hutu sune shikashikanmu
Karanci a gurin nema mun raina samuwar mu
Bacci a daure taya zamu gane safiyar mu
Wai ina abunda kake tanazarwa kanka gobe
Wai ina abunda kaima gobe za a maka obey
Wai ina abunda kake tattalawa mabiyanka
Ina shiri na kunya da zaka bawa mabiyanka
Kodadai ancewai zafin nema baya kawo samu
Amma rashin fita ke saka rabonmu ya gujemu
Kifin dake cikin ruwa zai tsallake kasarmu
Abunda muke gudu shi zai mamaya kasarmu
To kaicho da irin rayuwar da mukeyi da kanmu
Babu gammo muke shirin dora tsaunika a kanmu
Acikin rashin sani munata mutuwa da ranmu
To mu tashi kan mu tsinci talata a larabar mu
Wannan gargadi ne gaduk wani matashi irina
Mata maza gajeru kokuma dogaye zubina
Ni mu gudu tare mu tsira tare shine nufina
Kodadai nasan kalilan ne zasu karbi tayi na
In kaki jin bari to ai duniya makaranta
Zata kasheka sannan ta sakaka a makaranta
Kai babban yaro bakaso ama karanta
Lokacin da zaka gane ka dade da makaranta
Cire tsoro fita nema mana haba jan namiji
Saka kwazo sa tinani mana kan ka zama miji
Kaida ba mace ba haba maye naka na jan aji
Kwadago ba yawa bane kawai dan ka shiga aji
Saboda haka yanzu shawari ne a gareka
Koka gyara koka bata amma dai ya rage naka
To idan kuwa kakiji ka tsaya wai saidai a baka
Kanaji kana gani a tsere tana ta rigaka
Kaiko dan uwa mai yasa kake rayuwa ta maye
Saboda rashin tunane kasa kanka shaye shaye
To shawara ta a gareka a yanzu kai a waye
Ka guji abunda zaka saka iyaye hawaye
To yan uwa shekarar dubu biyu da ashirin
Gayawa sunusi umar nasir dashi da a shirin
Zainab maryam rukky laila duk ku kasance a shirin
Zuwa inda alama take yi mana al bishiri
Kai wai kidan ta kareh
Miss ai ban gama isar da sakona ba aii
Cash media record