Shawara Lyrics
- Genre:World Music/Folklore
- Year of Release:2022
Lyrics
Ya Rabbi Allah mai haska kowa
Kai keda komai kai ke rabawa
Kabani da'ma ka tausaya'wa
Rayuwa ta don ban iyawa
Mmm don ban iyawa
Rayuwa ce ni ban da kowa
Ba'ni da dawa koko maiwa
Ya kai hujja ake kafawa
Har wasu ma su kire ni wawa
Su kire ni wawa
Da yardan saidul baraya
Allahu sarki zai bude hanya
Inda tuo ba mucinsa gaya
Alfarman uban rukayya
Mmm uban rukayya
Ashe azuci sam basu sona
Gulma sukeyi akan lamari na
Da sun zauna sai dai batuna
Ai kunga sun zamo munafiquna
Mmm munafiquna
A'rayuwa wai wa zaya soka
Yabi tabaya yana bacinka
Fari da baki rigar hankaka
Ba marin mu a'hana mu kuka
Mmm a'hana mu kuka
Manzon Allah yafada
Muso junan mu har abada
Mubar jayayya da hassada
Ruwan soyayya mu kwankwada
Mu kwankwada
Don Allah yan'uwa maza da mata
Mu ajiye komai ga shawara ta
Mu gane cewa duniya da kanta
Tanada karshe mu dau fahimta
Mu dau fahimta
Nace mu dau fahimta
Mmm mu dau fahimta