Aure Da Kudi Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2018
Lyrics
Aure Da Kudi - Babangida Kakadawa
...
…..
Yau naayi tagumi na rame ban iya cin komai
Allah koro
Allah koro da Masoyiya ta
Rashin ganinta na rame bana iya cin komai
Yau ga dan talakawa yana son yar mai kudi
In na biya sadaki ni baza nayi laifi ba
Da na biya sadaki ni baza nayi laihi ba
Idan taje gida na bazan barta a tsumma ba
Da Da’am man watakil lallai babanta baya so ba mamarta bata so ba
Matan garin ga sunyi yawa kuma sun cika tunbulbul
Kuma basu son aure sai sun bidi mai kudi
Idan baka da kudi bana baza ka yi mata ba
Idan kana da kudi in sun ganka da mota har hotuna suke kaima
Darji bidi mai kwari
Tsoho da kudi yaro, yaro in ba kudi yau ya koma tsoho
…..
Ana wata magana jama’a ga wata magana ta zo
Wani ya mai jaki ya ingiji mai goyo babbar magana annan
Ji ana wata magana jama’a ga wata magana ta zo
Wani mai jaki ya ingiji mai goyo babbar magana annan
Ji samari na son mata kuma sannan ba kudi
Gayu na son mata bana gayu ba kudi
Sai xama a kan hanya da takama da sa Tshirt
Sai zama a kan hanya da takama da sa 2pac
In sun ka ga mata wadansu na fadin cika
Wasu na fadin chizga
Muna nan muna aikin baza mu tsayawa ba
In ka ga tsayawa ta sai in mutuwa ta zo
Babangida kakadawa mai kida kanin sani
Na dan maraya wakar ba kayi sai mu
Duka zare yana tsinke banda irin nawa
Dan nawa zaren da ya murde ya zama karfen jirgi
Kirar sa sai makeran asali suyi ka horo nai
Gamu,
Dan da dan haye da dan gado baza su zame daya ba
Hmm
Yaro bai san yaro nai ba
Yaro bai san yaro nai ba
Sai ya rasa baba nai ko ya rasa mama tai zai san yaro ne shi
Kuji dai yana ganin duniyar nan tai masa talala wai har da fadin wai sune zasuyi ba mu ba
In banda rashin kunya
Mai bidar nama mi ya kai shi zuwa gulbi kuma har da yukake nai
Mai bidar kifi mi ya kaishi zuwa kwata miya kaishi zuwa zango kuma harda zugun taru
Tsohuwar kura mai bidar kashin bango
Wancan na kan gina
In ta kai mai tsoka baza ta raga mai ba
Tsohuwar kura sai dai kici kanki
Ni ba za ki ci na ba
Yalummmmm
Alhaji Babangida kakadawa mai kida kanin sani
Na dan maraya wakar uwa kayi sai mu
Yau nayi tagumi na rame ban iya cin komai
Ga dan talakawa ya na son yar mai kudi
Da ya biya sadaki ni baza nayi laifi ba
Idan taje gida na
Bazan barta a tsumma ba