- Genre:World Music/Folklore
- Year of Release:2020
Lyrics
Talaka - Babangida Kakadawa
...
Yau nayi tagumi
Na rame ban iya cin komai
Allah koro
Allah koro da masoyiyata
Rashin ganin ta na rame
Bana iya cin komai
Yau ga dan talakawa
Yana son 'yar mai kudi
In na biya sadaki
Ni bazana yi lehe ba
Dana biya sadaki
Ni bazana yi lehe ba
Idan taje gidana
Bazan barta a tsuma ba
Dada amma watakil lale
Babanta baya so ba
Mamarta bata so ba
Matan garin ga sunyi yawa
Kuma sun cika tunbul-bul
Kuma basu son aure
Sai sun bidi mai kudi
Idan baka da kudi
Bana baza kayi mata ba
Idan kana da kudi
In sun ganka da mota
Har hotuna suke kaima
Garje bidi mai kwari
Tsoho da kudi yaro
Yaro inba kudi
Yau ya koma tsoho
Ana wata magana jamma'a
Ga wata magana tazo
Wani mai jaki ya in'giji mai goyo
Babbar magana a nan
Ji ana wata magana jamma'a
Ga wata magana tazo
Wani mai jaki ya in'giji mai goyo
Babbar magana a nan
Ji samari
Mai kida kanin Sani
Na Dan Maraya
Wakar wa kayi sai mu
Dukan zare yana tsinkewa
Banda irin nau wa
Don nau zaren daya murde
Ya zama karfen jirgi
Kirarsa sai makeren asaili
Su yi ke horo nai, ga mu
Don da dan haye da dan gado
Ba zasu zame dai ba
Yaro bai san yaro ne ba
Yaro bai san yaro ne ba
Sai rasa baba nai
Ko ya rasa mama tai
Zai san yaro ne shi
Kuji dai yana ganin duniyar nan
Tai masa talala harda fadin
Wai sune zasuyi bamu ba
In banda rashin kunya
Mai bidar nama
Mi ya kai zuwa gulbi
Kuma hada yukake nai
Me bidan kifi
Mi ya kai zuwa kwata
Me yakaishi zuwa zango
Kuma harda zugun taru
Tsohuwar kura
Mai bidar kashin bango
Wachan mai kan gina
Inta ga mai tsoka
Bazata raga mai ba
Tsohuwar kura
Sai dai kici kanki
Ni baki cina ba, yalum
Alhaji Babangida Kakadawa
Mai kida kanin Sani
Na dan Marayan
Wakar wa akeyi sai mu
Yau nayi tagumi
Na rame ban iya cin komai
A'a ga dan talakawa
Yana son 'yar mai kudi
Dana biya sadaki
Ni bazana yi lehe ba
Idan taje gidana
Bazan barta a tsuma ba