![Dake](https://source.boomplaymusic.com/group10/M00/07/09/a85ac0f526724e0e97c445123aecbe8a_464_464.jpg)
Dake Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2024
Lyrics
Cikin zuciata inai dake
A Rayuata ma sai dake
Mai bani Yanci in sha rake
Ni sai dake zana shallake
Ga hannuna taho rike
Ka jani duk inda so yake
A lamarin sonka ban sake
Ga wani rami taho cike
Zan kalli teku ni bangani ba kece idanun dake jikina
Kinada iska da zanyi rayuwa matso en shaqa abar yabona
Kibani kunnenki yar'uwata kidanji zancen dake gurina
A baya kinzama farin cikina yanzu kece farin idona
Abadan kece ruwan jikina wallahi ba wata kamarki guna
Da kayi dariya da kayi kuka a zuciya ba kamar ya kai
Da kayi wake ko karatu bazanji muryar da tai ya kai
Cikin mafarki ko a zahiri ni ban ganin wani daidai da kai
Ko kana kusa ko kana nesa zuciya ba a fidda kai
Kai dai nake da hange gareni ka take duk matakai
Gaba gaba gun walwala ta kuma kece silar damuwa ta
Ke na zaba da rayuwa ta ko da mutuwa
Dadin da ke da dadi masoyiyar rai jini da hanta
Kaunar dake da kauna kin bani so haka ni na wadata
Dake daya raina na yarda da za'a banke ni na azurta
A ko da yaushe abun yabona a ko ina baka canza suna
A qoramar sonka nayi niisa nagaza haaure ta maigidana
Edan da haske a zuciyataaa_soyayya eta na dandana
Shi ajiyar so akwai wuya dan ba'a ganinsa a ko ina
Enbaka dama Kabani daama mu dama rayuwa tare da juuna
Baza'a so ni ba en baki sona bazanaso ba en bada ke ba
Sannan en rayuwa en qara rayuwa en qara sau dubu ke naka duba
Da zuciya ta alqibla ce ako da yaushe ke zana duba
Dani dake gidanmu zamuje ae badan dake ba bazanaje ba
Enbaki dandanon albishiri rayuwar gidanki bada kishiyaa ba
Samun masoyi alheri ne rashinka wannan babbar illa ce
Da kai nai farko dakai nai qarshe edan na sameka nayi dace
Dauke ni sahibi dakai na yarda ajjeni daji ni na amince
Igiyar aurenka zan riqeta alqawarin sonka na rubuce.
Ae dole enyiwa Allahu godia da arziqinsa na kere zance