Intro (Maya Hai'huwa) Lyrics
- Genre:Gospel
- Year of Release:2024
Lyrics
Nasami maya hai'huwa
Nasami maya hai'huwa
Nina sami
Maya Hai'huwa
Nasami Maya Hai'huwa
Littafi mai tsarki yayi koyarwa
Akan maya hai'huwa
Cikin littafin yahaya sura uku daga
Aya ta farko, lokacin da babban malamin nan
Ya ziyarci Yesu Almasihu da dadare
Domin ya nuna masa goyan bayansa dakuma
Karbar sa a asirce
Yesu ya tabbatar masa cewa
Muddun ba'a maya hai'huwar saba toh bazai
Gaji mulkin Allah ba
Wannan maya hai'huwa ina nufin
Samun chanji wanda ruhun Allah yake kawowa a zuciyar mutum
Duk wanda yace ya bada gaskiya ga Yesu Almasihu, toh muddun an maya hai'huwarsa zakaga
Chanji acikin rayuwarsa wato wannan maya hai'huwa yasamu kyakyawan chanji ne acikin dabi'u da halayansa
Toh dan haka maya hai'huwa tanada mahimmanci kwarai da gasken gaske acikin rayuwar mai bin Yesu Almasihu
Ah Maya Hai'huwa ruhu mai tsarki yake
Maya hai'huwar mutum idan mutum yaba da gaskiya ga Yesu ya bude zuciyar sa ruhu mai tsarki ya shiga
Ya dauki jagoranchin rayuwar toh daga nan
Maya Hai'huwa zata tabbata
Duk wani rayuwa dazai yi zata zama domin ya daukaka Ubangiji ne
Kamar yanda bulus manzo acikin Galatiyawa sura biyu aya ashirin, yace rayuwar danake yanzu ina rayuwa ne domin in gamshi Yesu Almasihu ba rayuwa ta kaina nake ba amma rayuwa ce domin Yesu Almasihu
Yesu ne ya ceceni
Ya tsamoni daga duho
Nasami maya hai'huwa
Yesu ne ya ceceni
Ya tsamoni daga duho
Nasami maya hai'huwa