![Gida](https://source.boomplaymusic.com/group10/M00/11/15/05745ba0bdf842a5ae520cae5e491e52_464_464.jpg)
Gida Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2023
Lyrics
Idan na tuna da gida
Sai in ji ni na fara hawaye
Idan na tuna da gida
Sai in ji da ina a bakin kofa
I miss many many things at home
I miss fura da nono
I miss girkin mama na
Kunun nan har da gurasa
Taliyar Hausa da masa
Dan su komai zan fasa
Dole ne na je gida
Ni kam zani je gida
Zani koma can gida
Duk wanda ya bar gida
Shi gida zai bar shi
Dole ne na je gida
Ni kam zani je gida
Zani koma can gida
Duk wanda ya bar gida
Shi gida zai bar shi
Ba kamar gida don nan ne muka tashi
A jiki na tabbas ka na da wani sashi
Barin ka na na sukar jiki na kamar mashi
Yabon ka dole ne fa babu fashi
Ina wadanda basu garin su
Ina wadanda can aka baro su
Ina wadanda annuba ta kore su
Ina ga wadanda dole ce ta kai su
Asalin kowa ai shi ne tushe
Kar ka ji shayin wai wasu zasu kunshe
Idan ka ki naka toh wallahi kayi mushe
Kamar mataciyar bishiya za ka bushe
Dole ne na je gida
Ni kam zani je gida
Zani koma can gida
Duk wanda ya bar gida
Shi gida zai bar shi
Dole ne na je gida
Ni kam zani je gida
Zani koma can gida
Duk wanda ya bar gida
Shi gida zai bar shi
Hmmm hmmm
Hmmm hmmm
Hmmm hmmm
Hmmm hmmm
Dole ne na je gida (zan koma)
Ni kam zani je gida (zan dawo)
Zani koma can gida
Duk wanda ya bar gida
Shi gida zai bar shi
Dole ne na je gida (zan koma)
Ni kam zani je gida (zan dawo)
Zani koma can gida
Duk wanda ya bar gida
Shi gida zai bar shi