
Muda Masoyan Mu Lyrics
- Genre:Acoustic
- Year of Release:2022
Lyrics
Muda Masoyan Mu - Auta mg boy
...
Bugaminni tambari
Zanyi tsokachi
Komai da lokachi
Dagaske
Naga anyi tanadi
Babu addadi
Dan kara gargadi
Adauke
Idan duniyache
Sai kaban dashe
Yau zamu rakkashe
Da maggi
Duniyarnan
Bamu zauna ba
Wanda kaso
Baimaka kaunaba
Lahirar mu
Ita muke duba
Masu nufin sharri
Bakuyi dacheba
Allah kareni
Baza nakuddurche ba
Ni wanda ya soni
Da sonshi nake kwana
…
Allah kasomu
Komai kabamu
Badon halinmu
Kasa asomu
Akaunachemu
Duk ayarinmu
Yau rabbi gamu
Munzo dakanmu
Fata ankajimu
Karemu da nuna zamba
Ga en uwanmu
Ya zamma tsira garemu
Kowa zai soka soshi
Yau rayuwache
Ahakan muka tsinche kanmu
Achiki wasu zasu somu
Dan kudi garemu
Wasu kuma su aibatamu
Wasu za suyi mana kyauta
Dan suje su furta
Dan chin fiska garemu
Wasu kumma su somu Dan Allah
Su addu,a ba abun da zasu bamu
Mu wannan ya ishe mu
Tunda kukkasomu
Kukache kunji zakuyi mu
Duk sanda waninmu yaffito
Haka zakuso shi ko ba komai garemu
Allah sarkin sarauta
Shike da iko ya debi na wani ya dauka
Duk wani aiki da zakai
Toh kakama Allah
Zakaga chi gaba gareka
Nima yau wakanake
Achiki an kasanni
Gashi na dada daukaka
Ba boka babu tsuggu
Ni narikke Allah
Allah shine me duka
Allah karemu en tsiya
Masu chi da addini
Allah kabasu shiriya
Wasu masu bakar anniya
Rokona me duka
Suma da kabasu shariya
Duk wanda ya kama hassada
Rokona me duka
Shima abashi shiriya
Duk wani mai kauche hanya
Allah Ina bara da abashi shiriya
Nima mai laifine Allah na rokeka fatana abani shiriya
Hanya daya muyi ta taffiya
Zango daya babu wariya
Dukka musulmi na duniya
Allah na rokeka da kabamu shiriya
Allah kabamu shiriya
Ahhh…..