So Ruwan Zuma Lyrics
- Genre:Acoustic
- Year of Release:2022
Lyrics
So Ruwan Zuma - Auta mg boy
...
Soyayya ruwan zuma, tafi ace ruwan guba
In kin sha ki ban na sha, kai tsaye babu fargaba
Kece a duniya ta soyayya, bani na baki mu raba
Jani muje kawai ki kai ni, zana taho da tsaraba
Ina sanki kin sani
Kullum shi nake tini
Indai babu ki babu ni
Soyayya ta ja mini
Lele nayi marhaba, da zuwanki ina farin ciki
Na shirya muje gurin, aureki in nai yi babu saki
Da dadi ka so a soka, nidai tawa na rike
Soyayya dani dake, babu abun dazai raba
Ni bazana barki ba
Ba zan so watan ki ba
Bazan kemace ki ba
Ni bazan guje ki ba
Ki sanya a ranki nine, mai kaunarki tun a da
Mai kushenki babu shakka, zan tatse kamar gyda
Duk mai son yaja dani, to ya fito ya jadada
Don tsabar ina da kishi, ko kallonki bani so ayi
Ina son zama dake
Ba ranar rabo dake
Komai nawa sai dake
Ni kaina kin mallake
Amanata ta zuciyata, kunki kawai na sallama
Don mun zamo jini da hanta, sanki kawai na karrama
Ko sunanki in naji, a take a take sai tsuma
Na bayar da rai gareki, ya zam fansa masoyiya
Ki samar da lokaci
Harda abunda zamu ci
Ina da wani tsokaci
Akan so nawa ni dake
Kece kadai cikon muradi na
Wace na mallaka wa sirri na
Na soki chan ciki a ruhi na
Ki zama ni na zama ke kauna
Kiji kadan cikin bayyani na
Aurenki ne kawai muradi na
In dai akanki ne, ina shiryu
Ko kainawa za'a datsewa
Bani da so dayafi naki
Yarda ki bani lokacin ki
Yanzu nazo kawai na ganki
Murmusa da zuciyarki
Ba sanadin da zana bar ki
Sai dai mutuwa tazo ta dauki
Da zata nemi izini, ta daukan ke kawai ta bar ki