- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2020
Lyrics
Mama - Adam A Zango
...
Adam A Zango
MAMA
Mama ayye-ayye
Mama ayye-ayye
Mama wayyo
Mama iye
Mama uhmm
Mama oh-oh
Mama
Kin rikirkita min tunani na
Kai son ki ya shiga kalbi na
Mama yee, Mama yee
Ya Mama hasken rai na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee, Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Mama ayye-ayye
Mama ayye-ayye
Mama wayyo
Mama iye
Mama uhmm
Mama oh-oh
Mama
Kai mabiyin duka waka ta
Kara sauti kan murayan ka
Watarana a daki na
Ina a kwance katifa na
Amo nake ji na tashi
Ashe kara ne na waya na
Sai na firgita na tashi
Na farka bacci na zauna
Sai nace, "Waye wannan yake ta faman damu na?"
Sai na dauka na duba ba number kuma ba suna
Na canza fuska nayi tsaki na kara jawo bargo na
Nan na koma na kwanta don bacci ne a idanuna
Na riga na sha aiki ga gajiya a gabobi na
Sai na sake jin sabon kara yana ta kuskure kunne na
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rai na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Ku tsaya kuji dan gina
Shin wai wake damuna
Baya ko jin tausayi na
Don ya hana inyi bacci na
Na duba kuma ba suna
Yana shiga mini hakki na
Mama yee Mama yee
Sai na dau waya ta na danna
Sannan na kara a kunne na ("Hello")
Sallama bisa tsarina
Shin wai wake damu na?
Sai tace "Adam Zango
Wa'alaika masoyina
Abin tunanin ruhi na
Ai yanzu zaka ji suna na"
Sai tace "Nice mama, yanzu zaka ji sirri na"
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rai na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Mama yee mama yee
Kin rikir kita min tunani na
Kai son ki ya shiga kalbi na
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rai na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Mamaye mamaye
Saboda dadin muryarta
Sai na goge idanuna
Nayi godiya gun Allah na
Don naji ta fadi sunana
Mamaye, Mamaye
Sai tace "Adam Zango
Nima halittar Allah ce
Ba kamar ka ba mai sona"
Sai nace "baiwar Allah
Mai kike nema guna?
Waya baki fa lamba na
Kika kasa kiran rana
Sai cikin dare kika damu na?"
Mamaye mamaye
Sai tace "Adam zango
Zan bayyana maka siffa na
Kar ka tsorata mai sona
A hankali kaga hali na"
Mama yee mama yee
"Ni aljana ce ba shakka
Ammah ina da tsoron Allah na"
Sai na firgita dangina
Na kauda wayar a kunne na
Bacci na sai ya kare
Sai sake-sake a ruhi na
Sai nace "wayyo Allah, nayi gamo fa a harka na"
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rai na
Mamaye, Mamaye
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunarki ta shiga ruhi na
Mama yee mama yee
Harkar mutum ya sha kaina
Ga aljanu kuma na bina
Na kosa gari ma ya waye
Don in sanar da iyaye na
Mamaye mamaye
Da gari yayo haske
Nayi sallar Asubahi na
Al'ajabi kuji dangina
Na kasa karya kumallo na
Ga yunwa na damuna
Na kosa inga umma na
Mai share mini kuka na
In fada mata sirri na
Domin ta share hawaye na
Mamaye mamaye
Nayi wanka kuma na shirya
Na dau jakar computer na
Na dau mukullin mota na
Sannan na kulle dakina
Mama, mama (wayyo)
Naje na shiga mota na
Da sake-sake cikin raina
Ina ta tukin mota na
Na rasa me ke damuna
Mama, mama (eh, wayyo)
Na kunna sautin mota na
Domin ya debe kewa na
Sai naji ance "Zango na" cikin sifikun mota na
Mama, Mama
Nai maza na taba burkina
Jin muryarta a kunne na
Sai tace "Ni ce Mama
Karda ka tsorata mai sona"
Mamaye, Mamaye
Tace "Albishirin ka fa Zango na
Na zarce kowa son ka
Da tausayin ka a ruhina"
Saita bayyan siffar ta
Gata zaune a gefe na
Uhmm wayyo kaina
Kyakkyawa kuji dangina
Ina ma ku gane kwatance na
Naso na bayyana kyawunta
Ammah ya zarce tunani na
Mamaye mamaye (wayyo!)
Sai tace "Kaji Zango na
Kar kayi mamaki na
Ni yar Sarkin Aljan
Baba na kuma na sona
Ni da kai Adam zango
Muna nan tare cikin kauna
Zana barka fa zan koma
Ba zaka sake gani na ba
Sai dai ka dinga tunanina"
Mamaye mamaye
Sai ta bace daga fuska na
Ina nan zaune a mota na
Ammah kaunar ta ya shiga ruhi na
Mamaye, Mamaye
Wayyo Allah aljana yau tashiga ruhi na
Mamaye mamaye
Kin rikir kita min tunani na
Kai son ki ya shiga kalbi na
Mama yee, Mama yee
Ya mama hasken rai na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
lyrics by jhidhex